Monday 12th of October 2026
No record found
Politics / 2026-08-24 23:00:47

Gombe/Kwami/Funakaye: Dan Takarar APC, Mai Jama’a Kallamu, Ya Nemi Goyon Bayan Al’ummar Mazabar


Daga Adamu Ali Tongo

Bayan an bayyana Injiniya Dakta Usman Maijama’a Kallamu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen cike gurbi na mazabar Gombe/Kwami/Funakaye da za a gudanar ranar 19 ga Satumba 2026, ya yi kira ga magoya bayansa da masu biyayya ga jam’iyyar APC a jihar Gombe da su haɗa kai domin samun nasarar jam’iyyar.

Injiniya Mai Jama’a ya samu tikitin jam’iyyar ne bayan gudanar da zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a shirye-shiryen tunkarar zaɓen cike gurbin, inda rahotanni suka bayyana cewa ya samu ƙuri’u 27, inda ya doke sauran ‘yan takarar.

Injiniya Mai Jama’a ya yi wannan kira ne a wata hira da manema labarai bayan ya zama ɗan takarar jam’iyyar a ranar Asabar a Malam Sidi.

Fitowar Mai Jama’a a matsayin ɗan takara na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa a jihar Gombe ke ƙara kaimi wajen shirye-shiryen zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya, wadda ta kasance babu kowa bayan rasuwar tsohon ɗan majalisar mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye, Yaya Bauchi Tongo, a watan Yunin 2026.

Injiniya Mai Jama’a ya ce a shirye yake ya kawo wa al’ummar Gombe, Kwami da Funakaye ribar dimokuraɗiyya da ci gaba.

Ya kuma gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, shugabannin jam’iyyar da magoya bayansa bisa irin goyon bayan da suka ba shi a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Haka kuma, Injiniya Mai Jama’a ya nemi goyon bayan dukkan ‘yan takarar APC, magoya bayan jam’iyyar da kuma al’ummar Gombe, Kwami da Funakaye.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanya ranar Asabar, 19 ga Satumba 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbin. Zaɓen zai ƙunshi rumfunan zaɓe 903, yankunan rajista 31 da ƙananan hukumomi uku.

540 0

Comments

Leave a comment

Newsletter

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Kayi rajista

Muhimmai

Labarai / 2026-03-14 16:31:44
Al’ummar Dubai Sun
NEWS / 2026-06-15 13:45:39
NBA Frees Nine Inmates, R
NEWS / 2026-04-02 06:17:40
Gombe Police Officers Dem
NEWS / 2026-03-24 18:06:45
Gombe L-PRES Equips Six U
NEWS / 2026-03-14 16:26:38
Zakat & Waqf Foundati

Gombe Reporters

Gombe Reporters is an online channel based in Gombe.....

Quick Links

© Gombe Reporters.. All Rights Reserved.